FA Cup: Wigan ta yi waje da Man City

City vs Wigan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na biyu kenan Wigan tana yin waje da City a FA

Kungiyar da ke rike da kofin FA, Wigan Athletic ta doke Manchester City da ci 2-1 har gida, kuma karo na biyu kenan tana yin waje da City a gasar kofin FA.

A bara Wigan ce ta lashe kofin FA a Wembley lokacin data doke City, wannan karon kuma ta casa ta a filin wasanta na Ettihad.

Jordi Gomez ne ya fara zura kwallo a ragar City a dukan fenariti kafin a tafi hutun rabin lokaci, bayan an dawo daga hutu Wigan ta kara kwallo ta biyu ta hannun James Perch.

City ta saka matsi matuka har sai da Samir Nasri ya farke kwallo guda daya.

Wigan za ta kara da Arsenal a Wembley wasan daf da na karshe.