"Doke mu a FA bai kashe guiwarmu ba"

Manell Pellegrini Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tun farko kocin ya ce zai dauki kofuna hudu a gasar bana

Kocin Manchester City, Manuel Pellegrini, ya ce dokewar da Wigan ta yi musu da ci 2-1 a kofin FA ba za ta kashe musu gwiwa wajen kokarin lashe kofuna a kakar wasa ta bana ba.

Chelsea ta ba City -- wacce ta lashe kofin Capital One -- tazarar maki tara a gasar cin kofin Premie, ko da yake tana da kwantan wasanni uku da ba ta buga ba.

Haka kuma City za ta kara da Barcelona a kofin Zakarun Turai ranar 12 ga watan Maris; a wasan farko Barca ce ta doke City a Ettihad da ci 2-0.

Pellegrini ya ce, "Mun lashe kofi daya, muna da sauran fafatawa domin lashe kofuna har zuwa karshen kakar wasan bana.Farko dai mu fara doke Barcelona ranar Laraba, sannan mu lashe wasanmu uku mu koma zagorancin gasar Premier."