Za a kalli Premier ta Majigi a Afirka ta Kudu

Arsenal ManCity
Image caption Karon farko da za a kalli wasannin Premier ta majigi da yin kwalli da kofin

Magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar Premier a Afirka ta Kudu za su kalli wasannin Premier ta majigi a Johannesburg a karshen watan Maris.

Za a nuna wasanni biyar ciki har da karawa tsakanin Arsenal da Manchester City da za a nuna ta majigin a ranar 29 da 30 ga watan Maris, a filin Zoo Lake Sports Club, da zai dauki 'yan kallo 12,000.

Magoya bayan kungiyoyin Premier za su yi ido da tsofafin 'yan wasan Afirka ta Kudu Mark Fish da Lucas Radebe.

Haku kuma tsohon dan kwallon Liverpool Robbie Fowler da tsohon dan kwallon Chelsea Marcel Desailly za su halarci filin a karon farko.

'Yan kallo na da damar daukar hotuna da kofin Premier.