Zamu doke Bayern Munich - Wenger

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wenger na fatan doke Bayern a Allianz Arena

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce tarihin na tare da kungiyarsa na samun galaba a kan Bayern Munich a gasar zakarun Turai.

Kungiyar Bayern ta doke Arsenal daci biyu da nema a bugun farko da suka fafata a Emirates, kuma a ranar Talata su ne za su dauki bakuncin Gunners.

Wannan wasan tamkar maimaici ne a kan fafatawar da aka yi tsakanin kungiyoyin biyu a zagaye na biyu a kakar wasan da ta wuce.

Wenger ya ce "mun saba dasu saboda mun taba zuwa can muka doke su".

A halin yanzu dai Bayern ta samu galaba a wasanni 16 a jere a gasar Bundesliga a karshen mako a yayinda ita kuma Arsenal ta tsallake zuwa zagayen kusa da karshen a gasar cin kofin FA bayan ta doke Everton.

Karin bayani