"Mun ji kunya kan cinikin Neymar"

Rosell Neymar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mahukuntan Spaniya sun tuhumi Barcelona da kokarin kauce wa biyan kudin haraji.

Shugaban Barcelona Josep Maria Bartomeu, ya ce kungiyarsa ta ji kunya dangane da cinikin dan wasan Brazil Neymar.

Bartomeu, ya shaida wa sashin wasannin BBC cewa ba su saba ka'idojin musayar 'yan kwallo ba.

Bartomeu ya ce "Abin kunya ne duk da amannar mun aikata dai dai. Muna ganin mun yi abin da ya kamata, dukkan huldar da muka yi cikin gaskiya mu kayi, ta hanyar data dace."

Tun a watan Fabrairu aka zargi kungiyar da kokarin kin biyan haraji, yayin da wani alkali a Spaniya ya ce yana da hujjojin da za suci gaba da bincike kan musayar dan wasan.

Ana tuhumar Barcelona da kokarin kin biyan £7.58 miliyan, bayan sun sayo dan wasan Brazil daga Santos a watan Yunin bara.