NFF ta bukaci $7.2m don kofin duniya

Super Eagles Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption NFF na fatan samun kudin da za ta dauki nauyin tawagar kasar a kofin duniya

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta bukaci $7.2 miliyan, domin daukar nauyin 'yan wasan Super Eagles a gasar cin kofin duniya da Brazil za ta karbi bakunci.

Cikin kudin da NFF ta bukata ta ce za ta baiwa kowanne dan kwallo ladan lashe wasa $10,000 a karawar rukuni, da $12,000 idan suka kai wasan zagaye na biyu.

Sauran ladan wasannin sun hada da $15,000 a wasan daf da na kusa da karshe, $20,000 a wasan daf da na karshe da biyan $30,000 idan tawagar ta kai wasan karshe.

Haka kuma kowanne dan wasa daga cikin su 23 za a dinga bashi alawus na $200 kowacce rana, jumulla za a kashe $2.6 milliyan wajen biyan ladan wasanni da alawus din 'yan wasa tsawon kwanaki 32.

Abin da ya rage a uwar kudi za a biya masu horar da 'yan wasa da mataimakansu da kudin jirgi zuwa Amurka wajen Atisaye da kuma kudin otal da za su zauna a Brazil