Zenith ta kori kocinta Spalletti

Luciano Spalletti Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Duk da taka rawar da kocin ya yi a kungiyar bai hana ta sallame shi ba

Kungiyar kwallon kafa ta Rasha Zenith St Petersburg ta raba gari da kocinta Luciano Spalletti.

Kungiyar ta maye gurbinsa da tsohon dan kwallon Rasha Sergey Semak, mai shekaru 38, a matsayin rikon kwarya.

Spalletti, dan Italiya mai shekaru 55, ya koma Zenith ne a watan Disambar 2009, ya lashe kofunan Premier Rasha biyu da kofin FA da Super Cup.

Sai dai Zenith ta dawo matsayi na biyu a teburi, bayan buga wasannin satin da ya gabata, sannan Borussia Dortmund ta doke ta da ci 4-2 a kofin zakarun Turai wasan zagaye na biyu.