UEFA tana tuhumar Bayern Munich

Bayern Munich Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tuni Uefa ta tsananta bincike domin sanin matakan da za ta hukunta kungiyar

Bayern Munich za ta fuskanci hukunci daga hukumar kwallon Turai, sakamakon saka rubutu a wani kyalle da ya danganci Kosovo da magoyin bayan kungiyar ya sa lokacin da suke karawa da Arsenal

Jami'in kula da yada labarai na hukumar Pedro Pinto, ya ce tuni Uefa ta fara zama akan lamarin, da kuma tuhumar wani rubutun da ake ganin an ci zarafi tawagar Arsenal.

Pinto ya ce "dangane da cin zarafin Arsenal, tuni hukumar ta samu rahoto daga kungiyar kwallon kafa dake yaki da wariyar launi ta Turai."

Bayern Munich ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar kofin Turai, bayan da ta doke Arsenal gida da waje da yawan kwallaye 3-1.