Malawi ba ta fice daga neman shiga kofin Afirka ba

Walter Nyamilandu
Image caption Kasar ta ce bata ga dalilan da zai sa ta fice daga neman gurbin shiga kofin Afirka ba

Malawi ta ce bata fice daga rukunin kasashen da za su buga wasan neman gurbin shiga kofin Nahiyar Afirka da Morocco za ta karbi bakunci a shekarar 2015.

Tun farko an ruwaito cewar kasar na fama da rashin isassun kudin da za ta dauki nauyin tawagar shiga wasannin neman gurbin buga kofin Nahiyar Afirka da kuma gasar matasa 'yan kasa da shekaru 20 .

Har ma aka ce shugaban hukumar kwallon kafar Malawi Walter Nyamilandu ya ce "Ba mu da wani zabi illa mu hakura da shiga buga wasannin neman gurbin kofin Nahiyar Afirka.

"Amma za mu shiga gasar wasan matasa 'yan kasa da shekaru 20."

Sai dai ranar Laraba Nyamilandu, ya sanar da sashin labaran BBC cewa "Bamu fice daga wasannin neman gurbin kofin Afirka, kuma bamu da niyyar fice wa."