An dakatar da Labadie wasanni 10

Joss Labadie
Image caption Hukuncin da aka yanke masa ya yi iri daya da wanda aka yanke wa Luis Suarez

An dakatar da dan wasan Torquay Joss Labadie buga wasanni 10, tare da cinsa tarar £2,000, bayan da FA ta same shi da laifin cizon abokin karawarsa.

Lamarin ya faru ne a karawar da Chesterfield ta doke Gull da ci 3-1, kuma ba a hukunta Labadie a wasan ba.

Hukuncin da aka yanke wa Labadie iri daya ne dana Luis Suarez na Liverpool lokacin da ya ciji dan kwallon Chelsea Branislav Ivanovic, a kakar wasan bara.

Torquay ta ce tana tunanin ko za ta dauka ka kara.