Man City ta damu da raunin Aguero

Sergio Aguero Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan yana fama da jinya a kakar wasan bana

Manchester City ta ce ta damu da raunin da Sergio Aguero ya ji a karawar da Barcelona ta doke su da ci 2-1, a gasar cin kofin zakarun Turai ranar Laraba.

Sai sauya dan kwallon Argentina wanda ya zura kwallaye 26 a raga a bana aka yi, bayan an tafi hutun rabin lokaci a wasan da suka buga a Nou Camp.

Aguero, mai shekaru 25, wanda ya buga wa City wasanni 15 daga cikin 26, na fama da jinyar rauni a gwiwarsa da tsagewar tsoka.

Barcelona ta yi waje da City a gasar cin kofin Zakarun Turai, bayan ta zura mata kwallaye 4-1, jumullar kara wa da suka yi gida da waje.