Sturridge ya samu kyautar 'yan kwallo

Hakkin mallakar hoto premier league
Image caption Dan wasan Liverpool, Daniel Sturridge

Dan kwallon Liverpool Daniel Sturridge ya samu kyautar gwarzon dan kwallon Premier na watan Fabarairu.

Dan wasan Ingila mai shekaru 24 wanda ya samu irin kyautar a watan Agustan kuma a watan da ya gabata ya zura kwallaye biyar.

Haskarar da Sturridge ya yi ta kai Liverpool zuwa matakin na biyu a kan teburin gasar Premier ta bana.

Kocin West Ham, Sam Allardyce mai shekaru 59 shi ne ya samu kyautar a bangaren masu horadda 'yan wasa.

West Ham a cikin watan da ya gabata ta samu nasara a kan Swansea City, Aston Villa, Norwich City da kuma Southampton.

Karin bayani