'Zan tsawaita kwangila ta a Old Trafford'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Robin van Persie da David Moyes

Dan kwallon Manchester United Robin van Persie ya ce yanason tsawaita kwangilarsa a Old Trafford.

Dan shekaru 30 da haihuwa, wasu rahotanni sun nuna cewar ba ya dasawa da kocinsa David Moyes abinda ya sa ake zargin watakila zai bar kungiyar.

Amma a yanzu dan kwallon Holland din ya ce zai ci gaba da taka leda a United.

Yace "Gaskiyar magana ina jin dadin wasa a nan, kuma ina son in ci gaba da bugawa fiye da shekaru biyu masu zuwa a Old Trafford".

Karin bayani