Rafli ne ya juya mana baya - Mourinho

Jose Mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho bai ji dadin yadda Aston Villa ta doke su ba

Jose Mourinho ya soki alkalin wasa Chris Foy da juya musu baya, lokacin da aka kori kocin da 'yan kwallonsa biyu a wasan da Aston Villa ta doke su da ci 1-0.

An Kori Mourinho daga fili daf a tashi wasa, bayan da aka sallami 'yan wasansa Willian da Ramires tun farko.

Mourinho ya ce "Munyi matukar rashin sa'a da muka tsinci kanmu da alkalanci irin wannan da muka gani."

"Wannan ba kuskure ba ne daga alakalin wasa, illa yadda ya jagoranci wasan tun farkonsa ya zuwa karshensa."