Rivaldo ya yi ritaya daga buga kwallo

Rivalvo Brazil Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya fi yin suna a tsawon shekaru biyar da ya taka leda a Barcelona

Tsohon dan kwallon Barcelona da AC Milan da Brazil Rivaldo, ya sanar da yin ritayarsa daga buga kwallo yana da shekaru 41.

Zakaran kofin duniya a shekarar 2002, kafin ya yi ritaya yana buga kwallo ne a kungiyar Mogi Mirim, wacce ta ke buga rukuni na uku a gasar Brazil, kuma shi ne shugaban kungiyar da yake taka leda da dansa Rivaldinho mai shekaru 18 da haihuwa.

Rivaldo wanda ya lashe gwarzon dan kwallon kafa na duniya a shekarar 1999 ya ce "Tarihina a dan wasa mai taka leda ya zo karshe."

Dan wasan ya fara kwallo a kwararren dan wasa a shekarar 1991, ya buga wa Brazil wasanni 74 daga tsakanin shekarar 1993 zuwa 2003.

Rivaldo ya fi fice ne lokacin da yake Barcelona daga tsakanin shekarun 1997 zuwa 2002, ya kuma buga wasanni a kungiyoyi 14 daga kasashe shida daga Nahiyoyi hudu.