Lukman na fatan buga kofin duniya

Haruna Lukman Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan ya ce zai tada kai mi da nufin ya buga kofin duniya a bana

Dan wasan Dynamo Kiev Lukman Haruna ya ce yana fatan zai buga wa tawagar Super Eagles gasar cin kofin Duniya a Brazil.

Lukman mai shekaru 23, rabonsa da buga wa Najeriya wasa tun gasar cin kofin duniya da Afirka ta kudu ta karbi bakunci a shekarar 2010.

Dan kwallon ya ce yana da karfin gwiwar yadda yake taka leda a kungiyarsa, zai sa koci Stephen Keshi ya gayyace shi tawagar 'yan wasan Super Eagles da za su buga kofin duniya a bana.

Haruna ya shaida wa sashin wasanni na BBC ce wa "Na yi fama da jinyar raunuka amma yanzu na samu sauki, kuma a Shirye nake na wakilci kasata."

Dan kwallon ya koma Dynamo Kiev a watan Yunin 2011 daga Monaco.