'United za ta dade bata lashe gasa ba'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Tawagar 'yan wasan United

Tsohon dan wasan Ingila Danny Mills ya ce mai yiwuwa Kulob din Manchester United ya shafe shekaru 10 kafin ya sake lashe kofin gasar Premier.

Kulob din wanda a halin yanzu shi ne ke rike da kambun ya sha kashi hannun Liverpool da ci 3-0 ranar Lahadi kuma a halin yanzu shi ne na bakwai a teburin gasar.

A cikin wata hira da BBC, Mills ya ce "Kulob din zai dauki shekaru 3 zuwa 4 kafin kafin ya koma hayyacinsa. Sannan ka yi tunanin cewar kungiyoyin Manchester City da Chelsea da Liverpool za su kara kafin a cikin wannan lokacin’’.

Manchester United ta lashe kambun ne a bara da maki goma sha daya, amma tun bayan da aka maye gurbin David Moyes da Sir Alex Ferguson a zaman manajan Kungiyar sai ta fara rauni.

Karin bayani