FA: Ba zamu hukunta Joe Hart ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hart ya yi karo da Boyd

Hukumar kwallon kafa ta Ingila- FA ta ce ba za ta hukunta golan Manchester City Joe Hart ba, a sakamakon karonsa da dan wasan Hull City, George Boyd.

Hart da Boyd sun yi karon kai a wasan da aka fafata a filin KC, inda City ta casa Hull daci biyu da nema.

A lokacin wasan dai alkalin wasa ya baiwa Hart katin gargadi, abinda ya sa hukumar FA ta ce ba za ta ladabtar da shi ba.

Sai dai kawo yanzu FA din bata yanke shawarar ko za ta hukunta Vincent Kompany ba, sakamakon jan katin da aka baiwa dan kwallon saboda kayar da Nikica Jelavic.