'Nigeria ba ta ce min komai ba'

Image caption Anichebe bai buga gasar kofin duniya a 2010 ba

Dan kwallon Nigeria, Victor Anichebe ya ce kawo yanzu ba a ce masa komai ba game zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil.

Dan wasan mai shekaru 25 a baya ya dakatar da batun bugawa Nigeria kwallo don maida hankali a kan kulob dinsa na West Brom.

Kakakin tawagar Super Eagles, Ben Alaiya ya ce kocin tawagar Stephen keshi na saran Anichebe zai canza ra'ayinsa game da bugawa kasar kwallo.

Anichebe ya ce "Babu wanda ya tuntube ni game da bugawa Nigeria".

Anichebe ya bugawa Ingila kwallo a bangaren matasa kafin ya koma takawa Nigeria leda a watan Maris na 2008.

Kuma yana cikin tawagar kasar data samu kyautar azurfa a gasar Olympics a shekara ta 2008.

Karin bayani