Carroll ya yi mamakin faduwar Man Utd

Roy Carroll Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Carroll ya koma Man United ne daga Wigan kan kudi £2.5m

Mai tsaron gidan Olympiakos, Roy Carroll ya ce ya yi matukar mamakin yadda tsohon kulob dinsa, Manchester United ya yi kasa a kakar wasannin bana.

United ta kai hari sau daya ne kawai a karawar da Olympiakos ta cinye su 2 da nema a zagayen farko na gasar Zakarun Turai.

Gabannin zagaye na biyu da za a yi a Old Trafford a ranar Laraba, Carroll ya shaida wa BBC Radio 5 cewa "Ban taba ganin Manchester United bata samu dama irin haka ba, abin ya bani mamaki kwarai musamman yadda suka yi wasan."

Carroll ya yi shekaru hudu a Manchester daga 2001 zuwa 2005, kuma kulob din ya lashe gasar premier league a shekarun 2002 da 2003, kana ya dauki kofin FA a shekarar da ta biyo baya.