Zakarun Turai: Chelsea ta yi nasara

Image caption Chelsea ta zama kungiyar Ingila ta farko da ta samu wannan dama

Kungiyar Chelsea kai wasan gab da na kusa da na karshe na kofin Zakarun Turai bayan ta doke Galatasaray da ci 3-1.

A karawarsu ta farko a Turkiyya sun tashi 1-1,a karawar ta biyu kuma Chelsea ta ci su 2-0.

Jumulla wasa gida da waje Chelsea ta casa bakin nata 3-1.

Samuel Eto ne ya fara cin kungiyarta Didier Drogba minti hudu da shiga fili.

Sai kuma Gary Cahill ya kara ta biyu a minti na 42.

Karin bayani