Murray ya raba gari da kocinsa Lendl

Andy Murray da Ivan Lendl Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Murray ya ce zai yi tunani kafin sanin abin da zai yi nan gaba

Dan wasan Tennis mai daraja ta daya a Burtaniya, Andy Murray ya raba gari da kocinsa Ivan Lendl, bayan shafe shekaru biyu suna tare.

Lendl ne ya jagoranci Murray ya kaiga daukar kofinsa na farko a gasar US Open a shekarar 2012 da daukar lambar zinari a gasar Olympic da kuma gasar Wimbledon ta bara.

Murray ya ce "Ina godiya har abada ga Ivan, mun koyi abubuwa da dama a tafiyar da muka yi tare kuma hakan zai amfane ni nan gaba."

Game da rabuwar ga abin da shi ma Lendl ya ce "Lokaci ya yi da zai maida hankali kan wasu ayyukansa, ciki har da yin wasanni na duniya."