Zakarun Turai: Real Madrid ta yi gaba

Image caption Kwallon ta biyu ita ce ta 41 da Cristiano Ronaldo ya ci a bana

Real Madrid ta yi nasarar zuwa wasan gab da na kusa da karshe na Zakarun Turai bayan ta lallasa Schalke04 da ci 9-2 jumulla.

A haduwarsu ta biyu ran Talatar nan Real ta ci kungiyar ta Jamus 3-1.

Kuma daman a karawarsu ta farko a Jamus, Real din ta casa su da ci 6-1.

Cristiano Ronaldo ne ya ci kwallaye biyu a minti na 21 da kuma na 74 a karawar ta biyu.

Morata ne ya jefa wa Real kwallo ta uku a ragar bakin minti daya bayan Ronaldo ya jefa ta biyu.

Shi kuma Hoogland ya ci wa bakin kwallonsu daya a minti na 31.