An dakatar da Boyd na wasanni uku

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Lamarin ya faru ne bayan karon da 'yan wasan biyu suka yi da juna.

An dakatar da dan wasan gaba na kungiyar Hull City George Boyd na buga wasanni uku bayan an tabbatar da zargin da hukumar Kwallon Kafa ta Ingila ke yi masa na tofa wa Joe Hart Yawu.

Dan wasan mai shekaru 28 ya tofa wa golan Manchester City wato Joe Hart yawun ne yayin wasan da kungiyoyin biyu suka buga ranar assabar a filin wasa na KC stadium wanda Manchester City ta ci 2-0.

Alkalin wasan Lee Mason da masu taimaka masa duk ba su ga lokacin da Boyd yayi tofin ba a minti na 68 na wasan, amma kyamarori sun nada.

Boyd dai ya musanta yin tofin amma kuma bai yi nasara a karar da ya daukaka ba.

A yanzu ba zai buga wasanni uku na gasar Premier da kungiyarsa za ta buga da kungiyoyin West Brom, da West Ham da Kuma Stoke City ba.

Karin bayani