Hukumar FA na tuhumar Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya caccaki alkalin wasa

Hukumar kwallon Ingila- FA na tuhumar kocin Chelsea, Jose Mourinho bisa aikata ba daidai, bayan da aka kore shi a wasan da suka sha kashi a hannun Aston Villa.

Mourinho ya shiga cikin fili yana magana da alkalin wasa Chris Foy bayan da aka baiwa Ramires jan kati a wasan.

A cikin wasan dai an kori Willian shima.

An baiwa Mourinho zuwa ranar Litinin ya maida martani game da tuhumar.

Mourinho ya ce "ban san abinda yasa aka koreshi ba, na tambayi alkalin wasa yaki yi min magana".

Karin bayani