Doke Olympiakos ya karfafamu- Moyes

Image caption David Moyes

Kocin Manchester United David Moyes ya ce yana saran nasarar kungiyarsa a kan Olympiakos ta fardodo da su a kakar wasa ta bana.

Robin van Persie ya zura kwallaye uku a ragar Olympiakos a wasan da United ta kai zuwa zagayen gabda na kusada karshe a gasar ta zakarun Turai.

Moyes yace "Mun taka rawar gani, kuma ina ganin wannan kwazon zai bamu damar farfado da kimarmu a kakar wasa ta bana".

Moyes na shan suka a Old Trafford musamman yadda Liverpool ta lallasa su da ci uku da nema a gasar Premier a ranar Lahadin da ta wuce.

A yanzu haka dai Manchester United ce bakwai a kan teburin gasar Premier ta Ingila.

Karin bayani