Sergio Aguero zai ci gaba da jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sergio Aguero

Dan kwallon Manchester City Sergio Aguero ba zai buga wasansu da Manchester United ba saboda rauni.

Dan wasan mai shekaru 25 ya ji rauni a wasan da Barcelona ta doke City kwanaki tara da suka wuce.

Kocin City, Manuel Pellegrini ya ce watakila sai mako mai zuwa sannan Aguero zai koma taka leda.

Dan kwallon Argentina ya zura kwallaye 26 a kakar wasa ta bana amma ya yi jinya sau biyu.

A halin yanzu Manchester City ce ta biyu a kan teburin gasar Premier ta Ingila a yayinda Chelsea ke jan ragama.

Karin bayani