Mourinho zai kalubalanci hukumar FA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho

Kocin Chelsea Jose Mourinho ya ce zai kalubalanci tuhumar da hukumar kwallon Ingila ke masa na aikata ba daidai ba.

Ana tuhumar dan kasar Portugal din ne bayan da aka koreshi a wasansu da Aston Villa a ranar Asabar da ta gabata ne.

Mourinho ya shiga cikin fili don ya magantu da alkalin wasan Chris Foy bayan da aka baiwa Ramires jan kati.

Yace "Na yanke shawarar yadda zan maida martani kuma ba zan amince da tuhumar ba".

Mourinho nada dama har zuwa karfe 6 a ranar Juma'a don ya kare kansa.

Karin bayani