Arsenal ta kwashi kashinta a hannu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ce dai ke jagorancin teburin gasar da maki 69.

Sakamakon wasa na 1000 da Arsenal ta buga karkashin jagorancin Arsene Wenger bai zo wa kungiyar da dadi ba saboda yadda Chelsea ta lallasa ta da ci 6-0 ranar Assabar.

A cikin mintuna 7 na farko wasan ne Chelsea ta jefa wa Arsenal kwallaye biyu, ta kafafun Samuel Eto'o da Andre Schurrle.

A minti na 31 Eden Hazard ya ci kwallo ta uku ta bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-gida, bayan da Oxlade Chamberlain ya taba kwallo da hannu.

Oscar ne ya ci kwallo ta 4 da ta 5 a minti na 41 da 65; kafin Mohammed Salah ya ci ta 6 a minti na 70.

Wannan dai ita ce nasara mafi girma da Jose Mourinho ya samu a gasar Premier; kuma shi ne karon farko da Chelsea ta doke Arsenal da ci 6-0 a tarihi.

Karin bayani