Laifi na ne da Chelsea ta ci mu 6-0 - Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Da ma tsohon dan wasan Arsenal Stewart Robson ya dora laifin shan kashin kan kocin.

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce shi ne ke da laifin kashin ci 6-0 da suka sha hannun Chelsea ranar Assabar, wadda ya bayyana a zaman daya daga cikin ranakkun da yafi bakin ciki a tsawon aikinsa na kochi.

Wenger ya ce ya dauki alhakin kashin da suka sha a wasan wanda shi ne na 1000 da kungiyar ta buga karkashin jagorancinsa.

''Na yi ammana cewa ni ne ya kamata in dauki alhakin kashin da muka sha; amma kuma ban jin akwai bukatar a yawaita magana kan kura-kuran da muka yi saboda muna da wani babban wasa a ranar Talata'' Inji Kocin bafaranshe a cikin wata hira da BBC.

Arsene Wenger dai shi ne koci na hudu da ya rike wani kulob a Ingila har ya kai ga buga wasanni dubu daya, wato bayan Sir Matt Busby, da Dario Gradi da kuma Sir Alex Ferguson.

Karin bayani