Ba zan bari suka ta dame ni ba -keshi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Keshi dai shi ne Koci dan Afrika da ya taba kai kasashe biyu gasar cin kofin duniya.

Kocin Najeriya Stephen Keshi ya ce ba zai bari sukar da ake yiwa salon wasansa, da zaben 'yan wasa da kuma matakan da yake dauka ta sa ya canza ba.

Ya ce a cikin shekaru uku bai taba samun rashin nasara ba a wata gasa a matakin nahiyar Afrika; amma duk da haka ake sukar salon jagorancinsa.

''Muddin iyalina na so na, ina aiki na kuma ina lafiya kalau,to sauran abin ya biyo baya ba komai ba ne'' Inji shi.

Tsohon Kyaftin din na kungiyar Super Eagles, wanda ya karbin ragwamar kungiyar sa'adda take cikin wani mawuyacin hali a shekara ta 2011, ya mai do ma ta da martabarta da lashe Gasar Cin Kofin Nahiyar Afrika ta 2013 da kuma jagoranctar ta har ta samu cancatar zuwa Gasar cin Kofin Duniya.

Karin bayani