Gasar La Liga ta zama danya - Martino

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Messi ne ya ceci Barcelona a hannun Real Madrid

Kocin Barcelona Gerardo Martino ya ce 'yanzu aka soma' gasar La Liga ta Spain bayan da suka doke Real Madrid daci hudu da uku.

Lionel Messi ne yaci kwallaye uku, kuma a yanzu maki daya ne ya raba tsakanin Barcelona da kuma Atletico Madrid da Real Madrid wadanda ke matakin farko.

Martino yace "An koma farko gasar La Liga, damu za a fafata wajen lashe gasar".

Ya kara da cewar Mun yi amfani da damar mu ta karshe, da an tafi an barmu".

Yanzu dai Messi dan Argentina shi ne dan kwallo da yafi kowanne zura kwallaye a wasan 'El-Classico' wato wasan hammayya tsakanin Real da Barca.

Messi ya ci kwallaye 21 kenan a irin wasan kuma ya shiga gaban fitaccen dan wasan Real Alfredo Di Stefano.

Karin bayani