Alkalin wasa ne ya cuce mu- Ronaldo

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ronaldo da Di Maria bayan an tashi wasa

Dan kwallon Real Madrid Cristiano Ronaldo ya ce "hukunci mai daure kai" ne ya janyo suka sha kashi a hannun Barcelona da ci hudu da uku a filin Bernabeu.

Lionel Messi ya ci fenariti biyu cikin kwallaye ukun da ya zura abinda ya baiwa Barca damar samun nasara a wasan.

Ronaldo yace "Abin nada wuya mutane da dama basa son mu samu nasara, da Barcelona ta fita daga takarar lashe gasa".

Gwarzon dan kwallon duniya din ya kara da cewar "Watakila basa son Real Madrid ta lashe gasar La Liga ne".

Ronaldo shima ya zura kwallo daya a bugun fenariti.

Tun lokacin da alkalin wasa Alberto Undiano Mallenco ya kori Sergio Ramos saboda kayar da Neymar, alamu suka nuna cewar Barca ce za ta samu nasara.

Karin bayani