Bayern Munich ta dauki Kofi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern ta zama kungiya mafi nasara a gasar Bundesliga

Bayern Munich ta dauki kofin gasar Bundesliga ta Jamus karo na 24, wasanni bakwai kafin kammala gasar.

Kungiyar ta samu nasarar ce bayan da ta bi Hertha Berlin gida ta ci ta 3-1.

Toni Kross ne ya fara ci wa Bayern kwallon farko a minti 6, sai Mario Gotze ya ci t biyu a minti na 14.

Sai kuma a minti na 66 Hertha ta ci kwallonta daya da fanareti.

A minti na 79 Frank Ribery ya kara kwallo ta uku.

Bayern ta kammala wannan wasa na sati na 26 da maki 74.

Borussia Dortmund na ta biyu da maki 52, yayin da Schalke 04 ke da maki 51.