Karon battar birnin Manchester

Image caption Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin kociyoyin biyu

Kociyan Manchester United David Moyes da na Manchester City Manuel Pellegrini na duba yadda za su yi karon battarsu a Old Trafford Talatar nan.

Dukkanin masu horad da kungiyoyin biyu sun bayyana kakar farko ta Moyes a Man United da cewa tana da wuya.

Moyes dan yankin Scotland na fatan ganin ya saka irin gagarumin goyon bayan da ya samu da sakamako mai kyau.

Manuel Pellegrini ya bayyana David Moyes a matsayin me hali na gari.

Manchester City za ta yi wasan ne da kamfar maki shida tsakaninta da Chelsea ta daya amma kuma da bashin wasanni uku a gasar ta Premier.

Ita kuwa Manchester United ta na da kamfar maki 11 tsakaninta da matsayi na hudu a Premier, wanda zai ba ta damar zuwa gasar Zakarun Turai.

Sauran wasannin na Premier na ranar Talatar nan Arsenal za ta kara da Swansea, Newcastle kuwa za ta hadu ne da Everton.

Karin bayani