Man City ta kunyata Man United a gida

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shi ne karo na goma da Manchester United ta sha kashi a Premier a bana abin da bata taba sha ba.

Manchester City ta bi abokiyar hamayyarta Manchester United har gida ta lallasa ta 3-0 a gasar Premier.

Edin Dzeko ne ya fara daga ragar United dakika 43 da fara wasa.

Sai kuma a minti na 56 ya kara ta biyu kafin Yaya Toure ya kara ta uku a minti na casa'in.

Da wannan nasara maki uku ne ya rage tsakanin Man City ta biyu da Chelsea ta daya a Premier.

Manchester Cityn kuma tana da sauran wasanni biyu da ba ta yi ba.

A sauran wasannin Premier din da aka yi Arsenal da Swansea sun ta shi 3-3.

Yayin da Everton ta bi Newcastle har gida ta jefa mata 3-0.

Karin bayani