Moyes ne ya fi dacewa- Charlton

Image caption Sir Bobby Charlton ya yarda cewa United ba ta yi wasa da kyau ba matuka a bana

Tsohon kwararren dan wasan Manchester United, Sir Bobby Charlton, ya ce Manchester United ta yi daidai da ta nada David Moyes kociyanta.

Tsohon dan wasan me shekaru 76, ya ce duk da koma bayan kungiya a bana, ba wai za su sauya komai da komai ba.

Ya kuma kafe cewa ba shakka sun yi zabin mutumin da ya da ce.

Sir Bobby Charlton ya kara da cewa wasan kwallon kafa abu ne da ke juyawa.

Saboda haka ba za a dauki lokaci me tsawo ba da za su sake dawowa sama a Premier.

Tsohon dan wasan na United da kuma Ingila Charlton, ya na Malaysia domin bikin ba da kyautar wasanni ta duniya ta Laureaus.

Kuam ya ce ya ji dadi baya nan za a yi wasa tsakanin United da City, sabo da yana zakuwa sosai akan wasan hamayya.

Manchester United yanzu tana matsayi na bakwai yayin da ya rage wasanni takwas a kammala gasar Premier.