Fulham ta sake daukan Diarra

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diarra ya buga wa Fulham wasanni 19, inda ya ci kwallo sau daya.

Kungiyar Fulham ta sake sabunta kwantiragin tsohon dan wasan Real Madrid Mahamadou Diarra har zuwa karshen kakar wasannin bana.

Dan wasan me shekara 32 ya koma kungiyar ne a watan Fabrairu na 2012 amma ya ji rauni a guiwarsa a shekarar.

Kwantiragin dan wasan na tsakiya na farko zai kare ne a bazarar da ta wuce, amma duk da sakinsa da kungiyar ta yi, ya ci gaba da atisaye da ita don ya murmure.

Fulham na da maki hudu daga matsayin mun tsira a gasar Premier, yayin da ya rage wasanni bakwai a gama gasar.

Ranar Lahadi za ta kara da Everton kafin ta hadu da Aston Villa da Norwich.