Kewell zai yi ritaya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kewell ya buga wa kasarsa wasa sau 58, kuma tun 2013 yake a kungiyar Melbourne Heart.

Tsohon dan wasan Leeds da Liverpool Harry Kewell ya sanar da shirinsa na barin wasan kwallon kafa.

Kewell dan kasar Australia me shekara 35, ya yi wa kungiyoyin biyu wasan Premier sama da 250 tsakanin 1995 da 2008.

Haka kuma ya dauki kofin Zakarun Turai da na FA da Liverpool a 2005 da 2006.

Wasansa na karshe zai kasance ne wanda kungiyar tasa ta yanzu za ta yi da Western Sydney Wanderers a gasar A lig ranar Asabar 12 ga watan Afrilu.

A shekarar da ta wuce ya je kasarsa da nufin sa shi cikin tawagar 'yan wasan da za su je gasar Kofin Duniya, bayan ya je ta 2006 da 2010.

A wata kuri'a da aka yi ta 'yan wasa da magoya baya da 'yan jarida a 2012 sun zabe shi a matsayin dan wasan da ya fi kowane dan wasa a tarihin kasarsa.