F1 za ta karrama fasinjojin jirgin Malaysia

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban filin tseren Razlan Razali ya ce, ''muna sane gasar babba ce duk da yanayin makoki da muke ciki.''

Za a karrama fasinjojin jirgin saman Malaysia da ya bace a yayin babbar gasar tseren motoci ta Formula 1 da za a yi ranar Lahadi a Malaysia.

Jirgin da ya taso daga Kuala Lumpur zuwa Beijing dauke da mutane 239, ya bace ne ranar 8 ga watan nan na Maris kuma ana kyautata zaton ya fadi a teku.

Kafin fara gasar tseren motocin za a yi shiru na minti daya kuma direbobi za su sanya wasu rubuce-rubuce a jikin motocins da kuma hulunansu na kwano.

Sama da 'yan kallo 84,000 ne suka halarci filin tseren me daukar 'yan kallo 120,00 a bara, amma kuma a wannan karon ana ganin kashi daya bisa uku ne na adadin jumullar 'yn kallon za su halarta.