Leekens ya zaman kocin Tunisia

Image caption Georges Leekens

Tunisia ta nada dan kasar Belgium Georges Leekens a matsayin sabon kocin tawagar 'yan kwallonta a yarjejeniyar shekaru biyu.

Tsohon kocin Belgium da Algeria mai shekaru 64, aikinsa na farko shi ne ya tsallakar da Tunisia zuwa gasar cin kofin Afrika da za a buga a shekara mai zuwa a Morocco.

Leeken ne ya jagoranci kasar Belgium zuwa gasar cin kofin duniya a shekarar 1998, kuma ya ja ragamar kasar har zuwa shekara ta 2012.

Tunisia ba ta nada sabon kocin ba tun lokacin da ta kori Ruud Krol bayan da kasar ta kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin duniya da za a buga a Brazil a bana.

Karin bayani