Morocco 2015: Eritrea ta janye

Image caption Tutar kasar Eritrea

Hukumar kwallon Afrika-CAF ta tabbatar da cewar kasar Eritrea ta janye daga buga wasan neman gurbin zuwa gasar cin kofin nahiyar da za a buga a Morocco a shekara ta 2015.

Ya kamata a Eritrea ta kara Sudan ta Kudu a zagayen farko na wasan share fage, amma kuma a yanzu Sudan ta Kudu za ta kai zagaye na gaba.

Eritrea ba ta bada hujja ba ta janye wa daga gasar ba, amma hakan bai rasa nasaba da kauracewar wasu 'yan wasanta.

A shekara ta 2012, 'yan wasan Eritrea 17 suka fice daga gasar SECAFA inda suka nemi mafaka a Uganda.

Sudan ta Kudu a karshen watan Afrilu za ta san da kasar da za ta fafata a zagaye na biyu.

Karin bayani