Zamu lashe gasar Premier - Rodgers

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Rodgers na jinjinawa magoya bayansu

Kocin Liverpool Brendan Rodgers ya ce tawagarsa za ta jurewa matsin lamba don lashe gasar Premier ta Ingila a bana.

Liverpool ta lallasa Tottenham daci hudu da nema a ranar Lahadi kuma za ta iya lashe gasar idan har ta samu galaba a wassaninta shida da suka rage a gasar ta bana.

Rodgers yace "Bama fuskantar matsin lamba kuma ina da tabbas zamu iya lashe gasar".

A yanzu dai Liverpool ce a saman teburin gasar inda ta shiga gaban Chelsea da Manchester City.

A cikin watan Afrilu, Liverpool za ta dauki bakuncin Chelsea da Manchester City a filin Anfield.

Rabon Liverpool ta lashe gasar Premier tun a shekarar 1990.

Karin bayani