Victor Valdes ya tafi jiyyar watanni 7

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Valdes zai bar Barcelona idan kwantiraginsa ya kare a kakar bana.

Mai tsaron gidan Spain da Barcelona Victor Valdes ba zai yi wasa ba tsawon watanni bakwai bayan da aka yi masa tiyata a guiwarsa.

Hakan na nufin golan ba zai je gasar cin Kofin Duniya da za a fara a watan Yuni me zuwa ba, wadda za a yi a Brazil.

Mai shekara 32, Valdes ya ji rauni ne a wasan da Barcelona ta yi nasara a kan Celta Vigo da ci 3-0, a makon da ya wuce.

A ranar Litinin aka yi masa tiyata a Jamus, kuma Barcelona ta tabbatar ba zai yi wasa ba sai akalla zuwa watan Oktoba.

Golan wanda ya bayyana aniyarsa ta barin kungiyar tun a kakar da ta wuce ya yi mata wasanni 535 tun da ya shige ta sama da shekaru goma.

Ya yi nasarar daukar kofunan La Liga shida da na Zakarun Turai uku da kuma na Copa del Reys biyu da Barcelonan.

Yana kuma daga cikin 'yan wasan Spain da suka dauki Kofin Duniya a 2010 da Kofin Kasashen Turai na 2012.

Rashinsa na nufin golan Real Madrid Iker Casillas da na Napoli Pepe Reina da kuma na Man United David De Gea za su nemi gurbinsa a tawagar Spain da za ta je gasar Kofin Duniya.