Atletico Madrid ta rike Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan shi ne karo na hudu da Barcelona ke yin canjaras da Atletico Madrid a bana

Atletico Madrid ta rike Barcelona a wasan dab da na kusa da karshe da ci 1-1a Nou Camp.

Diego ne ya fara daga ragar Barcelona bayan an dawo daga hutun rabin lokaci a minti na 56.

Barcelona ta rama cin ta hannun Neymar minti 71 da wasa.

Atletico Madrid na da dama fiye da Barcelona a karawa ta biyu da za a yi a Madrid saboda kwallon da ta ci.

Wannan shi ne karo na hudu da kungiyoyin da ke hamayya a La Liga da kofin Zakarun Turan ke yin canjaras a bana.

Rabon da Atletico Madrid wadda za ta karbi bakuncin Barcelona ranar Laraba me zuwa ta zo wannan matakin na gasar tun 1997.