Brazil: An dakatar da aiki a filin wasa

Filin wasa na Beira-Rio a Brazil Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Karo na uku kenan ana samun mutuwar masu aiki a filin wasan

Jami'an gwamnatin Brazil sun dakatar da aikin gine-ginen wucin gadi, a filin wasan da za a yi gasar cin kofin duniya.

Hakan ya biyo bayan mutuwar wani magini a filin wasan Itaquerao, a Sao Paulo a ranar Asabar data gabata.

A wannan filin wasan ne za a yi fafata wa ta farko a gasar cin kofin duniya da za a fara a watan Yuni.

Ana fargabar cewa dakatarwar za ta haifar da karin matsaloli ga masu shirya gasar, ganin dama can an samu jinkiri a aikin filin wasan.