Liverpool za ta biya Portsmouth idan ta dauki Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayan shekaru biyu a Portsmouth Liverpool ta sayi Glen Johnson a kan fam miliyan 17.5

Me yuwuwa Liverpool za ta biya Portsmouth fam miliyan daya idan ta dauki Kofin Premier saboda Glen Johnson.

A yarjejeniyar cinikin dan wasan a 2009, Portsmouth ta ce idan Liverpool ta dauki Premier za ta biya ta wannan karin kudi.

Johnson me shekaru 29 ya koma Portsmouth ne daga Chelsea a 2007 bayan zaman aro.

Sai dai ba a sani ba ko har yanzu wannan sharadi yana nan ganin cewa kungiyar ta Portsmouth ta samu sauyin masu mallakarta.

Liverpool tana ta daya a Premier yayin da ya rage wasanni shida a kammala gasar.

Ita kuwa Portsmouth tana ta 21 a gasar League Two, tana da maki biyar tsakaninta da fadowa kasa.