Damuwar Man United a wasa da Bayern

Image caption David Moyes ya ce, ''yan wasan suna cikin natsuwa, ni kuma na zaku mu yi wannan wasa.''

Manchester United na fama da matsalar rashin lafiyar 'yan wasan baya yayin da take shirin wasan kofin Zakarun Turai da Bayern Munich.

Daga cikin matsalolin nata, Patrice Evra ba zai buga ba saboda an dakatar da shi.

Kuma akwai shakkun amfani da wanda zai iya maye gurbinsa Alexander Buttner saboda raunin da ya ke jiyya na cinya kamar yadda Rafeal shi ma ke fama.

A kwanan nan ne dai Rio Ferdinand da Jonny Evans da kuma Chris Smalling suka murmre daga raunukan da suka ji.

Juan Mata ba zai buga ba saboda ya fara buga wasannin gasar a Chelsea kafin ya koma Man United.

Kociyan kungiyar, David Moyes, ya ce, kakar wasannin nan ta kasance me wuya a gare su amma za su yi kokari su ba d mamaki in har suka yi nasara a wasansu na Talatar nan.

Ita ma Bayern Munich ba za ta sa Thiago Alcantara ba saboda raunin da ya ji a guiwa.

Alcantara me shekaru 22 ba zai yi wasa ba akalla tsawon makwanni shida sabod raunin da ya ji a wasansu da Hoffenheim ranar Asabar.

Karin bayani