'Yan hukumar FA ta Uruguay sun ajiye aiki

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Magoya bayan Nacional sun yi dauki-ba-dadi da 'yan sanda bayan da kungiyarsu ta yi rashin nasara ran Laraba.

Dukkanin mambobin hukumar zartarwar kwallon kafa ta Uruguay sun ajiye aiki saboda matsalar rikici a filayen wasanni.

Jami'an sun dauki wannan matakin ne a cewarsu, domin su bai wa wasu masu ra'ayi na daban su taka rawarsu a shugabancin harkar kwallon kasar.

A makon da ya gabata Shugaba Jose Mujica ya hana tura 'yan sanda tsaro a filayen wasan Penarol da Nacional saboda rikici.

Kungiyoyin biyu su ne fitattun manyan kungiyoyin kwallon kafa biyu na Uruguay.

Duk da janye 'yan sandan hukumar ta umarci kungiyoyin biyu su cigaba da wasanninsu kamar da amma 'yan wasan suka ki.