FIFA ta dakatar da Barcelona

Image caption Wannan dakatarwar za ta iya shafar makomar Barcelona

An dakatar da zakarun kwallon Spain, Barcelona na tsawon watanni 14 daga sayen 'yan kwallo saboda saba doka wajen sayen 'yan wasan da suke kasa da shekaru 18.

Hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA ce ta dakatar da Barcelona, inda a yanzu kungiyar ba za ta iya kara sayen 'yan kwallo ba har sai zuwa bazarar shekara ta 2015.

Haka kuma an ci tarar kungiyar ta Barcelona fan dubu 305.

Hukumar ta Fifa kuma ta dauki matakin ladabtar da hukumar kwallon Spain (RFEF) saboda saba ka'ida.

A don haka an ci tarar RFEF fan dubu 340 sannan aka bukace ta ta yi gyara game da yadda ake cinikin 'yan wasa a gasar kwallon kasar ta Spain.

Karin bayani